Gwamnatin Jihar Jigawa tace zata fara biyan sabon tsarin albashi mafi karanci a wannan watan na Disamba.
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar shi ya tabbatar da hakan lokacin da yake jawabi ga yan kungiyar kwadago reshen jihar jigawa bayan an yi yarjejeniya tsakanin yan kwadagon da Gwamnati a gidan Gwamnatin jihar.
A fadar Gwamnan, Gwamnatin Jihar da yan kungiyar kwadagon sun shiga tattaunawa a watanni biyu da suka gabata kafin a cinma yarjejeniyar tsakanin su.