
Kwamitin kare hakkin mai saye na jihar Jigawa yace ya kwace buhunhuna 14 na ridin da aka yiwa gauraye, na kimanin kudi naira Dubu 250, daga wani dan kasuwa mai suna Munkaila Alasan, a yankin karamar hukumar Gumel.
Gwamnatin jiha ce ta kafa kwamitin wanda zaiyi aiki da tallafin masu bincike wajen kame yan kasuwa wadanda ke algus a kayan amfanin gona, tare da gurfanar dasu a gaban kotun tafi da gidanka.
Shugaban Kwamitin, Mallam Faruk Abdallah, ya shaidawa manema labarai a nan Hadejia cewa, Munkaila Alasan ya gauraya ridin da kasa a cikin buhunhuna domin kara musu nauyi.
Yace an gurfanar da Munkaila Alasan a gaban kotun ta tafi da gidanka, karkashin mai sharia Mannir Sarki, wanda ya yanke masa hukuncin daurin watanni 18 ko zabin biyan tarar kudi ta naira dubu 75.
Shugaban kwamitin yace kotun ta bayar da umarnin lalata ridin da aka yiwa algus.
Yace kwamitin zai cigaba da tabbatar da cewa ba a sayarwa da mutane kayan da aka yiwa algus ba.