Fafaroma farancis ya hori shugabannin duniya da su kyale hasken kirsimeti ya ratsa duhun zukatan mutane wanda ke jawo kashe-kashe wanda ya shafi addini, rashin adalchi, rikice-rikice da makamai tare da kyamar ‘yan gudun hijira.
A sakonsa na ranar kirsimeti, fafaroman dan shekaru 83 a duniya, yayi kiran a samun zaman lafiya a kasa mai tsarki, da sham, da Lebanon, da Yemen da Iraqi da Venezuela da Ukraine da sauran kasashen Afirka da dama wadanda ke fama da rikice-rikice.
Babban jigon jawabinsa wanda yayi a gaban dubban mutane a dandalin Saint Peters da kuma miliyoyin mutane dake kallo ko sauraro a fadin duniya, shine canji yana farawa ne daga zukatan daidaikun mutane.
A ranar 1 ga watan Disamba, akalla mutane 14 aka harbe har lahira a wani harin da aka kaiwa wata coci a gabashin kasar Burkina Faso, inda yan ta’adda suka tayar da rashin jituwar kabilanci da addini.
Fafaroma Francis wanda yake shan suka daga yan siyasa saboda yadda yake kare yan gudun hijira, ya sadaukar da wani sashe guda na jawabin nasa wajen wahalwalun da suke fuskanta, inda yayi kira da a rufe guraren kulle yan gudun hijira a kasar Libya.