Babu Ranar Bude Iyakokin Kasarnan – Buhari

25

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace bai tsayar da ranar sake bude iyakokin kasarnan ba.

Yace iyakokin za su ci gaba da zama a rufe har sai yanayin da ake ciki ya inganta.

Shugaban kasar yace yawan man fetur din da kasarnan ke sha ya ragu da kashi 30 cikin 100 tun bayan da aka rufe iyakokin.

Kakakin Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu, cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, yace shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin da ya karbi tawagar dattawan jihar Katsina a gidansa dake Daura.

Shugaba Buhari yace gwamnatinsa na kokarin daukar matakan farfado da aikin gona a kasarnan.

Shugaban Kasar sai ya yabawa matakin da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Isufu, ya dauka na korar jami’ai tare da soke amfani da kasar wajen fasa-kwaurin kayayyaki zuwa Najeriya.

Shugaban yace matakan da kasar ta Nijar ta dauka suna taimakawa tare da tallafawa manufofin Najeriya.

Shugaban ya bayyana cewa yana sane da wahalhalun da al’umomin dake kusa da iyakokin kasarnan ke sha, sanadiyyar dakatar da sayar da mai a gidajen man garuruwan dake da nisan kilomita 20 zuwa iyakokin, matakin da ya hana sayar da mai a garinsa na Daura.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =