Asusun UNICEF ya Tantance Mata Masu Juna Biyu 323 Domin HIV a Bauchi

151

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kaddamar da shirin tantance mata masu juna biyu a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 323 a jihar Bauchi ga masu cuta mai karya garkuwar jikin tare da bada Magani kyauta ga mutane da suke da cutar.

Shugaban ofishin hukumar a Jihar Bauchi Mista Bhanu Pathak shine ya bayyana haka ga manema labarai akan aikace-aikacen hukumar.

Ya ce hakan wani mataki ne na hana yaduwar cutar daga mata masu juna biyu zuwa ga yaran da suke ciki.

Kazalika ya ce hukumar ta samarda magunguna kyauta ga cibiyoyi 323 da suke fadin jihar.

Haka kuma ya nanata kudirin hukumar na hadin gwiwa da gwamnatin jihar domin ganin sun inganta rayuwar raya kanana.

Kazalika hukumar ta bawa ma’aikata 1,200 horo kan yadda zasu rika taikamawa mutanen da suke zaune a kyauyika domin bada agajin da yakamata.

Ya ce jami’an zasu rika taimakawa wajen kula da marasa lafiya kamar zazzabin cutar Malaria da Gudawa da kuma sauran cututtuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 2 =