An dakatar da jami’ai 7 na hukumar gyaran da’a bisa laifin kashe fursunoni 5 da wutar lantarki

18

Hukumar Dake Kula da Civil Defense, Gidan Gyaran Da’a, Kashe Gobara da Shige da Fice, ta amince da dakatar da manyan jami’ai 7 na hukumar gyaran da’a ta gidan yari, bisa laifin kashe fursunoni 5 da wutar lantarki a Ikoyi, Lagos.

An kuma dakatar da wani karamin jami’i bisa abin takaicin da ya auku.

Kakakin hukumar, Mista Francis Enobore, wanda ya shaida haka cikin wata sanarwa a Abuja, yace dakatarwar tazo ne domin samun gudanar da sahihin bincike akan lamarin.

Francis Enobore yace takardar dakatarwar ta samu sahalewar sakataren hukumar, Mallam Hassan Yakmut.

Yace jami’an da lamarin ya shafa, an dakatar da su, har zuwa lokacin da kwamitin ladaftarwa na hukumar zai kammala bincike.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa, shugaban hukumar gidajen gyaran da’a, Mallam Ja’afaru Ahmed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan kisan mutane 5 da wutar lantarki a babban gidan yarin Ikoyi dake Lagos, a ranar 2 ga watan Disambar da muke ciki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + sixteen =