Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tace ‘yan gudun hijira 43 aka mayar jamhuriyar Nijar daga kasar Libya.
Kwanaki kadan baya, hukumar ta bayyana mayar ‘yan gudun hijira 306 zuwa Rwanda daga kasar ta Libya.
Hukumar tayi kiyasin cewa ‘yan gudun hijira 4,500 da masu neman mafaka ne suke tsare a cibiyoyin ajiye mutane a kasar Libya, inda ta tabbatar da cewa suna fuskantar barzanar rikicin da ake yi zai shafe su.
Dubban ‘yan gudun hijira ta haramtacciyar hanya, yawancinsu ‘yan Afirka, suke tsallaka ruwa daga Libya zuwa Turai, sanadiyyar halin rashin tsaro da rikici a kasar da ke Arewacin Afirka, biyo bayan tumbuke tsohon shugaban kasa, Muammar Ghaddafi a shekarar 2011.
Dakarun Sojin Tawayen Libya da gwamnatin kasar wacce ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, na gwabza yaki tun farkon watan Afrilu, akan iko da babban birnin kasar, Tripoli, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane dayawa wadanda suka hada da ‘yan gudun hijira.