Daga Kawu Sule Rano
Tare da girmamawa da ladabi ga Mai Martaba Sarki, Allah ya taimaki Sarki, Allah ya karawa Sarki lafiya.
Allah ya taimake ka wannan wasikar na rubuto tane domin bada shawara game da kalaman Sarki kan badakalar satar yara kanana ‘yan asalin jihar Kano da aka bankado a kwanankin baya.
Sabanin yadda naji Mai Martaba ya fahimci abin, da yawan yaran nan da aka sace ba shekarun su uku ba wasu ma sun kai shekaru 7 zuwa takwas, sannan ba yawon bara suke ba lokacin da aka sace su.
Dadin dadawa ran Sarki ya dade, mafi yawan masu satar yaran nan fa mata ne dake iya shiga har cikin gidaje, su faki numfashin iyaye tare da yin awun gaba da yaran su.
Don haka, Allah ya taimaki Sarki, a gaskiya mu talakawa baza mu taba fahimtar ka ba, musamman da kace wai da kana da gwamnati daka daure iyayen yaran nan, saboda a fahimtar daka nuna “sakacin” su yaja aka sace yaran. Ran Sarki ya dade kalaman sunyi tsauri musamman a kunnuwan iyayen da aka sacewa yaran nan nasu, dama na mu talakawa dake karkashin ku.
Ko da yake, ban sani ba ko Mai martaba ya bincika ne ya gano cewar sakacin iyayen yaran ne ya haifar da sace wadannan yara. Amma kuwa ranka shi dade, baka ganin cewa sace yaran nan nada nasaba da dabaru, hikimomi, gogewa wasu lokutan ma siddabaru da barayin yaran ke amfani da su?
Bari in bada misali, Mai martaba Sarki, Allah ya taimake ka, wanne sakaci zaka alakanta da matar da ta shiga wanka aka shiga har cikin gidanta aka sace mata yaro kafin ta fito? Menene sakacin ta anan don Allah?
Ka tuna, Ranka shi dade, Allah ya taimaki Sarki, wannan fa Najeriya ce, kasar da ku shugabanni kuka fifita tsaron lafiya data dukiyar da kuka mallaka fiye da tsaron rayukan al’ummomi da kuke mulka. Na tabbata ko kasar Nijar din nan ta fimu nuna damuwa da tsaron mutanen ta.
Alal misali, ranka shi dade, jami’an tsaro nawa ke gadin gidan ka? Jami’an tsaro nawa ke bin tawagar motocin ka idan zaka unguwa? Jami’ai nawa ke rakiyar mata da yaran ka? Naga har gunduma guda (divisional police command) ke gidan ka, a matsayin ka na sarki, don Allah ku nawa ne a gidan? Don Allah ka taba neman gwamnati ta rage yawan wadannan jami’ai dake tsaron lafiyar ka, saboda a samu damar bada cikakken tsaro ga lafiya da dukiyar talakawan dake karkashin masarautar ka?
A wannan kasa da kuke mulka abin ya kai, duk da irin tsaron da kuke ba kan naku ma, ana iya sace manyan jami’an soji, dana ‘yan sanda, kai harma da manyan sarakunan masu daraja ta daya da manyan hakimai an sata yafi a kirga, kuma amafi yawan lokuta, ba tare da kun iya damko masu laifin ba, to anan kuma wa za’a hukunta kenan?
Allah ya taimaki Sarki ni shawara zan bada, idan har ku manyan mu da muke alfahari daku ba zaku bamu kariya ba, to don girman Allah kada ku ringa yin kalaman da zasu rage kima da mutuncin mu a wajen abokan zama. Ranka ya dade watakila baka da labarin Anacha (Onitsha) da kayi magana akanta sosai, amma ina tabbatar maka da cewa sun dade suna fama da matsalar satar yara tun kafin ma abin yayi tsamari anan.
Ina fatan Mai martaba zai duba wannan shawara ya kuma janye kalaman sa, sannan ayi koyi da Mai Martaba Sarkin Bichi, Alh. Aminu Ado Bayero wajen jajantawa iyayen da aka sacewa yaran su sannan kuma da cigaba da kokarin kare masu haddin su da aka keta.
Ina fatan Allah ya karawa Mai Martaba Sarki lafiya da tsawon rai mai amfani, amen.
Kawu Sule Rano, ya aiko da wannan wasika daga Jihar Kano.