Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da hukumar wata kungiyar ilimi mai suna Pearson Educational Group a Birnin Landan

40

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da hukumar wata kungiyar ilimi mai suna Pearson Educational Group, a Birnin Landan.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa mai bawa shugaban kasa shawara na musamman shine ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a Abuja.

Kakakin shugaban kasar, wanda ya kuma dora hotunan ganawar a shafin nasa, yace ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, da sakataren zartarwa na hukumar jami’o’in kasarnan, Farfesa Abubakar Rasheed, sun halarci ganawar.

Femi Adesina ya kuma ce, jakadan Najeriya a Ingila, Justice Adesola Oguntade, ya samu halartar ganawar.

Kamfanin na dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, a ranar Lahadi, shugaban kasar ya gana da Archbishop na Canterbury, Most Reverend Justin Welby, a fadar Lambeth dake birnin Landan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − thirteen =