Shugaba Buhari Zai Bar Abuja Gobe Juma’a Zuwa Kasar Equatorial Guinea

42

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja gobe Juma’a domin halartar taron kasashen dake fitar da iskar gas karo na 5 a Birnin Malabo, na kasar Equatorial Guinea.

Kakakin Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu, shine ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

A cewar sanarwar, bayan shugaba Buhari, taron na wuni guda zai samu halartar shugabannin manyan kasashe mafiya arzikin iskar gas a duniya.

Kasashen sune Algeria, da Masar, da Equatorial Guinea, da Libya, da Bolivia, da Iran, da Qatar, da Russia, da Trinidad and Tobago, da Daular Larabawa, da Venezuela, da Kazakhstan da kuma kasar Norway.

Garba Shehu yace wadannan kasashen su ke da kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na arzikin iskar gas a duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + seven =