Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da kyautar gaskiya da amana ga wasu ma’aikatan gwamnati 2, Bashir Abubakar, ma’aikacin hukumar hana fasa kwauri ta Customs da Mrs Josephine Ugwu ta hukumar jiragen sama na Najeriya, bisa nuna gaskiya da adalchi yayin gudanar da ayyukansu.
Manema labarai sun bayar da rahoton cewa, shugaban kasar ya gabatar da kyaututtukan ga mutanen yayin bude taron kasa na kwanaki 2 akan raguwar rashawa a aikin gwamnati, wanda aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.
Taron, ofishin sakataren gwamnatin tarayya ne ya shirya tare da hadin gwiwar hukumar yaki da almundahanar kudade, ICPC.
Bashir Abubakar wanda mataimakin comptroller janar ne a hukumar ta kwastan, ya ki amincewa da karbar cin hancin kudi Dala Dubu 412, kwatankwacin Naira Miliyan 150 akan kowace kwantaina guda wanda wasu masu safarar kwaya suka bashi domin shigo da kwantaina guda 40 cike da kwayar tramadol.
Ita kuwa Mrs Josephine Ugwu, wacce tsohuwar mai shara ce a filin jiragen saman kasa da kasa na Murtala Muhammad dake birnin Lagos, a lokuta da dama ta sha mayar da miliyoyin kudaden da take tsinta yayin aikinta, ciki har da kudi Dala Miliyan 12 wanda wani matafiyi ya manta a wani bandakin filin jirgin.
Da yake jawabi yayin taron, Shugaba Buhari ya jaddada bukatar ‘yan Najeriya su dauki dabi’ar gaskiya da amana wadanda al’adun gargakiya suke martabawa.