Sanata Ali Ndume Ya Kaddamar Da Gidauniya Domin Tallafawa Dalibai 1000

38

Sanata Ali Mohammed Ndume na jam’iyyar APC daga jihar Borno, ya kaddamar da asusun tallafawa ilimi mai suna Ndume Education Trust Fund, domin tallafawa ilimin dalibai 1000 da suka fito daga kudancin jihar Borno, kuma suke karatu a makarantun gaba da sakandire daban-daban na jihar.

Ali Ndume, wanda ya bayyana haka yayin kaddamar da asusun a dakin taro na Elkanemi dake jami’ar Maiduguri, yace yayi haka yayin cikarsa shekaru 60 a duniya da kuma bashi dama wajen tallafawa rayuwar mutanen mazabarsa.

Yace an zabo daliban dake jami’ar Maiduguri da Ramat Polytechnic da jami’ar Jihar Borno da kwalejin ilimi ta Kashim Ibrahim, da Makarantar aikin jinya, da kwalejin aikin gona da sauransu, inda ya kara da cewa kowannen su zai samu kyautar kudi Naira Dubu goma-goma, karkashin asusun.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yabawa sanatan bisa kokarinsa na taimakawa jin dadin da tattalin arzikin jama’ar jihar.

Gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Usman Jidda Shuwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one + nine =