Masu Zabe Sun Jefa Kuri’a A Zaben Shugaban Kasa A Guinea Bissau

47

Masu zabe sun jefa kuri’a a zaben shugaban kasa na Guinea Bissau, a yau Lahadi, da burin cewa za a samu sauyi a kasar da ke fama da juyin mulki, biyan makonni ana rikicin siyasa da ya jawo tashe-tashen hankula tare da rufe majalisa.

Shugaban kasar Jose Mario Vaz, dan shekara 61, na neman zarcewa a karo na 2, kuma har yanzu yana da farinjini tsakanin manoman kashu, bayan ya kara farashin kwallon kashu, wanda shine babbar hanyar samun kudaden ‘yar karamar kasar dake yammacin Afirka.

Amma yana fuskantar kalubale biyo bayan zangonsa na farko wajen rikicin siyasa ya dabaibaye, da cin hanci da rashawa, wadanda sune lamuran da ake magana akai a zaben na yau.

Shugaban masu sa ido na tarayyar Afirka, Jaoquim Branco, yace an kada kuri’a da sassafe lami lafiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − 8 =