Kwastan sun kwace kaya na kimanin kudade sama da Naira Miliyan 43 cikin mako guda

29
Kanar Hameed Ali mai ritaya, shugaban hukumar hana fasa-kwauri

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya Custom, shiyyar Kaduna, tace ta kwace kayayyakin fasa kwauri na kimanin kudade sama da Naira Miliyan 43, cikin mako guda a shiyyar.

Kwamturola na shiyyar, Mustafa Sarkin-Kebbi, yace daga cikin kayyakin da aka kwace akwai wata babbar mota da aka tare akan titin Kebbi zuwa Kalgo, wacce ke dauke da shinkafa ‘yar waje da aka boye tare da takalman sawa cikin jakankuna masu nauyin kilogram 100.

Mustapha Sarkin-Kebbi, wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Kaduna, ya kuma ce an tare motoci 25 a makon, tare da buhunnan shinkafa 703, da jarkokin mai 500, da kuma katan-katan na taliya 245.

Sauran kayan da aka kwace sune diloli 9 na kaya gwanjo da jarkoki 40 na kalanzir, da wata babbar mota dauke da lita dubu 30 na man fetur da aka zuba a cikin jarkoki, a iyakokin kasarnan dake jihar Kebbi.

A cewarsa, duk da sumamen hukumar ta kwastan akan dakile fasa kwauri a shiyyar, tare da rufe iyakokin kasarnan, har yanzu masu fasa kwauri basu dena ayyukansu ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − three =