Hukumar kula da gidajen yari ta kame wata matashiya mai kai ziyara gidan yari a Jihar Kano

75

Hukumar kula da gidajen yari, reshen jihar Kano, ta kame wata matashiya mai kai ziyara gidan yari, wacce aka boye sunanta, a gidan yari a Kano.

Matar wacce ta kai ziyara, ana zarginta da kokarin shigar da kwayar da aka haramta zuwa gidan yarin.

Jami’in hukumar a Kano, Mallam Musbahu Lawan, wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa a Abuja, yace ana kyautata zaton kwayar Diazepam ce.

Musbahu Lawan yace wacce ake zargin, mai kimanin shekaru 20 a duniya, ta fito ne daga unguwar Hotoro, cikin yankin karamar hukumar Nasarawa na jihar ta Kano, kuma an kama ta da kwayar ta kimanin kudi Naira Dubu 300, yayinda take kokarin shigar da ita gidan yarin.

Yace an boye kwayar cikin miya, wacce akayi nufin kaiwa wani wanda aka kulle a gidan yarin yana jiran hukunci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 + twelve =