Gwamnatin Zamfara za ta hana yara yawon tallace-tallace a lokutan zuwa makaranta

298

Gwamnatin jihar Zamfara tace wata dokar dake gaban majalisar dokokin jihar zata hana yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta yawon tallace-tallace yayin lokutan zuwa makaranta a jihar.

Gwamnan jihar Bello Matawalle, shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya karbi kyautar girmamawa akan jin dadin malaman makaranta a Enugu.

Kungiyar shugabannin makarantun firamare a Najeriya ce ta bashi kyautar.

Bello Matawalle, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar ilimi bai daya a jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Maradun, yace gwamnati baza ta bar kowane yaro a bay aba, wajen kudirinta na tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingattaccen ilimi matakin farko a kyauta kuma tilas.

A cewarsa, dokar tana kuma kokarin tallafawa gwamnati wajen ganin cewa dukkan yaran suke shekarun zuwa makaranta, suna zuwa makarantar domin samun ilimi a matakin farko.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 − two =