GWAMNATIN TARAYYA KWANANNAN ZATA KADDAMAR DA AIKIN GINA BUTUTUN ISKAR GAS MAI TSAWON KILOMITA 600 DAGA AJAOKUTA ZUWA KADUNA ZUWA KANO

18

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatin tarayya kwanannan zata kaddamar da aikin gina bututun iskar gas mai tsawon kilomita 600 daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, wanda zai tafiyar da iskar gas daga kudanci zuwa arewacin kasarnan.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja, yace shugaban kasa ya bayyana haka yayinda yake jawabi a taron kasashe masu arzikin iskar gas karo na 5 wanda ake gudanarwa a dakin taro na kasa da kasa na Sipopo a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea.

Shugaban kasar ya kara da cewa ana kuma shawara kan yiwuwar mikar da bubutun na gas zuwa kasashen arewacin Afirka.

A cewar shugaban kasa, yarjejeniyar Paris ta shekarar 2015 ita ta assasa jajircewar kasashen duniya wajen wannan aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two − two =