Gwamnatin Kasar Zimbabwe Ta Kori Kananan Likitoci 435 Daga Aiki Saboda Shiga Haramtaccen Yajin Aiki

20
Zimbabwe's President Emmerson Mnangagwa looks on as he gives a media conference at the State House in Harare, Zimbabwe, August 3, 2018. REUTERS/Philimon Bulawayo

Gwamnatin Kasar Zimbabwe tace kawo yanzu ta kori kananan likitoci 435 daga aiki a asibitocin gwamnati, saboda shiga haramtaccen yajin aiki.

Likitocin na yajin aiki tun farkon watan Satumba, inda suke neman karin albashi tare da inganta yanayin aiki.

Kotun ma’aikata a watan Oktoba ta ayyana cewa yajin aikin bai hallata ba, amma sai likotocin suka yi kunnen kashi tare da cigaba da yajin aikin, inda suka nakasa ayyuka a manyan asibitocin gwamnati da cibiyoyin lafiya a kasar.

Hukumar kiwon lafiya ta kasar tana da sauran hukunce-hukunce 45 da zata yiwa likotocin.

Ministan yada labarai mai rikon kwarya, Mangaliso Ndlovu, ya shaidawa manema labarai cewa gwamnatin a ko da yaushe a shirye take ta tattauna da likotocin, kuma korarsu daga aiki shine matakin karshe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × two =