Gwamnatin jihar Yobe ta kirkiro bayar da tukwici na naira dubu 1 kan kowane irin bishiya da ‘yan sakai suka dasa

104

Gwamnatin jihar Yobe ta kirkiro bayar da tukwici na naira dubu 1 kan kowane irin bishiya da ‘yan sakai suka dasa kuma suka rena, domin dakile barazanar kwararowar hamada da gurbatar muhalli.

Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya bayyana haka a Damaturu, yayin biyan tukwicin ga wadanda suka amfana, yace sama da ‘yan sakai dubu 2 ne wadanda suka dasa bishiyoyi a fadin jihar za su amfana da kudin.

Mai Mala Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana, yace anyi hakan ne da nufin yaba kokarin jama’a wadanda ke agazawa kokarin gwamnati na dakile barazanar kwararowar hamada da gurbatar muhalli.

Gwamna sai ya umarci shugabannin kananan hukumomi, da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, da su dauki matakai wajen ingiza mutanensu su shiga shirin na dashen bishiya.

Daga nan sai Gwamnan ya godewa abokan hulda na kasa da kasa bisa shiga shirin yaki da barazanar kwararowar hamada da gurbatar muhalli.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × four =