Humukar alhazan Nijeriya tace ta samar da asusun gata ga masu son yin aikin hajji na shekarar 2020 domin basu damar biyan kudin aikin hajjin a hankali.
Shugabar sashen hulda da jama’a na hukumar alhazai Hajiya Fatima Usara ce ta bayya haka yayin da ta ke zantawa da manema labarai a Abuja.
Ta ce sun yanke shawarar samar da asusun gatan ne don bawa masu son zuwa sauke farali damar tara kudin aikin hajjin acikin sukuni, kuma ko wane maniyyaci shine zai zabi adadin kudin da yake so ya fara ajiyewa.
Hajiya Fatima ta yi kira ga alhazai da su rika basu bayanai bayan aikin hajji ta hanyar shawara ko korafi domin bawa hukumar daman inganta ayyukan su.