Ministan noma da raya karkara Sabo Nanono ya bayyana cewa Nijeriya nayin noman da zata ciyar da kanta harma ta tura shi kasashen ketare.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a jajibirin bikin ranar abinci na duniya a Abuja, inda ministan yace “Nijeriya nayin isashen noma da zamu iya ciyar da kanmu. Inaga babu yunwa a kasar, za’a iya samun damuwa dai. Idan naji mutane na cewa akwai yunwa a wannan gwamnati, abin yana bani dariya”.
A cewar ministan, abinci a Nijeriya yana da matukar arha ba kamar sauran kasashe ba. “A Nijeriya, abinci akwai arha. Zakaci abinci naira 30 kacal kuma ka koshi a Kano. Don haka sai muyi godiya tunda muna iya ciyar da kunmu kuma abincin mu akwai arha ” inji Nanono
Ranar abinci na duniya ana yinsa a fadin duniya ranar 16 ga watan oktoba na ko wane shekara domin tunawa da kirkiro hukumar ba da tallafin abinci na majalisar dinkin duniya a 1945.