APC tayi tir da harin da aka kai gidan Oshiomhole

63
Adams Oshiomhole

Jam’iyar APC tayi Allah wadai da harin da aka kai gidan shugaban jam’iar na kasa Adams Oshiomhole.

Harin wanda aka kai ranar Asabar da ta gabata ana zargin ‘yan barandan siyasa ne suka afkawa gidan shugaban jam’iyar na APC.

Acikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyar Lanre Issa Onilu ya fitar a jiya Lahadi, yayi tir da wannan abun takaici kuma ya bayyana harin a matsayin barazana ga rayuwar sugaban jam’iyar.

Mista Onilu yace yanzu haka ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin.

Sharhi 1

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =