An kubutar da yara 70 a Daura

202

Rundunar ‘yan sandar jihar Katsina ta bayyana kubutar da wasu mutane daga makarantar gyara halinka a garin Daura na jihar Katsina.

A yayin da ‘yan sanda suka kai mamaye a makarantar mallakin malam Bello mai almajirai, sunyi nasarar kubutar da mutane a kalla 70 wadanda suka hada da yara da matasa, da kuma wasu da shekarun su ya kai 40.

Bayanai sun tabbatar da cewa akwai yara sama da 300 a gidan marin na malam Bello mai almajirai, amma saidai mafi yawancinsu sun tsere yayin da ‘yan sanda suka kai mamaye a gidan, abinda yasa ba’a iya kubutar dasu baki daya ba.

Ko a kwanakin baya ‘yan sanda a Kaduna sunkai mamaye a irin wannan gida da ake kira na gyara halinka, amma kuma ake azabtar da yara inda sukayi na sarar kubutar da mutane masu dimbin yawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + 18 =