Zimbabwe: Ana zaman makokin mutuwar Mugabe

70
Robert Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya ayyana kwanakin makoki a kasar baki daya har sai an binne gawar tsohon shugaban Kasar Robert Mugabe wanda ya mutu ranar Juma’a a wata asibiti da ke kasar Singapore.  

Mnangagwa ya yabbayan kwanakin maokikin a cikin wata jawabi da yayi wa al’ummar kasar a jiya Jumma’a in da ya bayyana Mugabe a matsayin gwarzo kuma dan kishin kasa.

Shugaban Kasar na Zimbabwe ya godewa gwamnatin kasar Singapore da suka dauki nauyin kula da lafiyar Mugabe tun lokacin da yake asibiti daga watan Afrilu har zuwa rasuwarsa.

A baya, SkyDaily Hausa ta ruwaito cewa Mugabe yamutu yana da shekaru 95 a duniya, kuma shine shugaba na farko da ya jagoranci kasar bayan samun mulkin kai. Sai dai kuma a watan Nuwamba na 2017 sojoji suka kifar da gwamnatinsa bayan ya shafe shekaru 37 yana jagorantar kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 11 =