Zimbabwe: An daga jana’izar Mugabe

39

An dange bikin jana’izar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe har sai zuwa wani lokaci anan gaba.

Bayanin dage jana’izar ya fito ne daga bakin daya daga cikin iyalan marigayin mai suna Leo inda ya shaidawa jaridar Zimlive cewa dage jana’izar ya zama wajibi domin kuwa Mugabe babban mutum ne don haka dole ayi masa jana’iza irin ta gargajiya.

Mugabe babban mutum ne, don haka dole ayi masa jana’iza ta gargajiya. Har yanzu sarakunanmu basu gaya mana inda za’a bizne shi ba, kuma nima ban sani ba” inji Leo

A baya dai, SkyDaily Hausa ta ruwaito cewa Mugabe ya mutu a kasar Singapore yana da shekaru 95 bayan yayi jinya tun a watan Aprilu na wannan shekara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen − 6 =