Kotun sauraren kararrakin zabe a Kaduna ta ce Malam Nasir El-Rufai na jam’iyar APC shine wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Kaduna da akayi a watan Maris din 2019.
Kotun karkashin Alkalinta Ibrahim Bako ta bayyana haka ne a jiya Litini lokacin da ta ke yanke hukunci akan karar da dan takarar Jam’iyar PDP Isah Ashiru Kudan ya shiga inda yake kalubalantar nasarar da El-Rufai ya samu.
Kotun ta yi watsi da da karar saboda rashin ingantattun shaidu daga dan takarar jam’iyar PDP.
A nasa bangaren, Babban Lauya Abdulhakim Mustapha wanda shine ke kare Gwamna El-Rufai ya bayya gamsuwarsu da hukuncin inda y ace kotun ta gamsu cewa Isah ashiru bashi da cikakkun shaida da zai nuna cewa shine ya lashe zaben ba gwamna Nasir El-Rufai ba.
Jam’iyar PDP kuwa ta bakin shugabanta Mista Felix Hassan Hyet tace ko kadan basu ji dadin hukuncin kotun ba, inda kuma ya bayyana cewa zasu zauna da lauyoyin su domin tattauna hukuncin sannan su fitar da matsayinsu akan hukuncin.