Zaben 2019: Atiku ya daukaka kara a kotun koli

64
Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP a zaben 2019 Atiku Abubakar ya daukaka karar a kotun koli don kalubalantar hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a ranar 11 ga watan Satumba inda ta bawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nasara.

Atiku yana kalubalantar nasarar da kotun karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Garba da sauran alkalai hudu suka bawa Buhari a matsayin wanda yayi nasara a zaben 2019.

Tun da farko dai, Atiku yana kalubalantar cancantar Buhari ne inda yace ya gaza gabatar da shaidar kamala makaranta na sakandire ta WAEC.

Hukumar zabe ta INEC dai ta amince da takardan sakandire a matsayin mafi kankartar shaidar karatu da ake so mutum ya samu kafin tsayawa takarar wani mukamin siyasa a Najeriya, wanda a cewar Atiku, Buhari bai iya gabatar da irin wannan shaidar ba.

Atiku da jam’iyarsa ta PDP suna kalubalantar hukuncin ranar 11 gawatan Satumba a gaban kotun Allah ya isa.

Sharhi 1

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + twelve =