Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke a wajen zaben fidda gwani na PDP

40

Hatsaniya ya tashi a wajen zaben fidda gwanin jam’iyar PDP a jihar Bayelsa inda kayi zargin yan bindiga sunyi musayar wuta da jami’an tsaro.

Harbe harben da ke gudana kuma ya fara wuce gona da iri ya tursasa jami’an zabe, yan jarida da sauran al’umma arcewa domin tsira da rayukansu.

Har yanzu dai babu cikakken dalilin da ya haifar da harbe harben a wajen zaben fidda gwanin da zaiyi wa jam’iyar PDP takara a zaben gwamna da za’ayi nan gaba kadan a jihar ta Bayelsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × three =