Daga Muhammad Lawal Gusau
Gwamnati a dukkan matakan iko, Kama daga na tarayya, jiha ko karamar hukuma suna kokari wajen Samar da shirye-shirye ko ace tsare-tsare Wanda zai samarwa Al’ummar da suke jagoranta cigaba ta fannin tattalin arziki, zamanta kewa da sauransu.
Irin wadannan tsare-tsare da gwamnati kanyi a matakai daban-daban sun kasu gida uku.
- Gajeren zango (short term plan)
- Matsakaici (mid term plan)
- Dogon zango (long term plan )
Gajeren zango tsari ne wanda ya kunshi shekara daya zuwa biyu.
Tsari matsakaici shine wanda ya kunshi shekara uku zuwa biyar.
Inda dogon zango yakai tsare-tsare har zuwa kimanin shekara goma ko fiye da haka.
Akwai kuma tsari wanda ake kira “NATIONAL DEVELOPMENT PLAN” Wannan wani tsari ne wanda ainihin gwamnatin tarayya ke tsarawa musamman a kasar da ke amfani da Presidential system of government, wanda ya kunshi gwamnatin tarayya, Jihohi da kuma kana nan hukumomi.
Shidai National development plan mafi aksari anfi tsara shi a matsayin mai dogon zango tareda aiwatar dashi ta hanyar wani yanayi da ake kira rolling plan.
Misali, lokacin General Olusegun Obasanjo sunzo da shiri mai suna “operation feed the nation”
A Najeriya tsohon shugaban kasa General Ibrahim Badamasi Babangida ya taba zuwa da shirin SAP wato “structural adjustment programme” wanda a lokacin yayi tasiri kwarai da gaske musamman ta bangaren farfado da noma domin bunkasar tattalin arzikin kasa wanda hakan yazamo sanadiyar kirkiro NAPRI Dake ABU zaria wanda har yanzu masu bincike a harkar Noma suna amfana da ita.
Haka zalika tsohon shugaban kasa Obasanjo yazo da shirye-shirye daban daban kamar su Poverty eradication programme, National economic empowerment programme and development da dai sauransu.
Marigayi Umaru musa ‘Yar’aduwa yazo da irin nashi salo na 7 point agenda. Inda daga bisani tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonthan yazo da Transformation agenda, wanda yayi kokarin farfado da tattalin arzikin kasa ta hanyar bada tallafi ga manoma da sauran bangarora na cigaban kasa.
A lokacin Jonathan ‘yan adawa na siyasa sun samu damar fadin albarkacin baki wanda dan adawa zaifito ya caccaki gwamnati iya son ransa, domin kuwa tarihi ya nuna ba’a tabayin shugaban kasa da ya sha zagi da suka daga ‘yan Najeriya kamar Jonathan ba. A zamanin mulkin Jonathan Malam Nasir El-rufa’i tare da Engr. Buba Galadima na daga cikin wadanda suka rika kalubalantar gwamnatin shugaba Jonathan wanda hakan ya tabbatar da akwai political development da kuma damar fadin albarkacin baki ga dukkan ‘yan kasa a wancan lokacin wanda hakan ya zama sanadiyar zaman Muhammadu Buhari shugaban kasa da akayi zabe cikin shekarar 2015.
Haka zalika Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi irin nashi kokari na kirkirar hanyoyi na bunkasa tattalin arzikin kasa kamar shirin Npower,YIEDP,GEEP, da sauransu.
Bisa ga wadannan shirye-shirye da suka gabata zamu iya cewa lallai tsare-tsaren kasa suna taimakawa sosai wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Amma fa dukkanin wadannan nasarori suna samuwa ne tareda gudummawar gwamnatocin jihohi.
A kowane lokaci gwamnatin tarayya tana gudanar da lamurran ta ne ta hanyar wannan tsari wanda ake kira National development plan.
Da wannan nake kira ga daukacin jihohin mu akan su bada gudummawar su ta amfani da shirye-shiryen da gwamnati ke samarwa tare da duba performance na kowane tsare-tsare da zasu taimaka domin kawo sauki ga al’umma tare da sauraren ra’ayin al’umma a duk lokacin da za’a tsara kowane shiri.
Ubangiji Allah yakawo ma kasar mu cigaba mai dorewa. Ameen
Activist Muhammad lawal Gusau