Tasirin Shafin Yanar gizo

219

Tare da Ahmad Bala

Shin ko ka san cewa mallakan shafin yanar gizo zai baka daman tallata aiyukan ka ko sana’ar ka a duniyar intanet ta hanya mafi tasiri?

Mallakan shafin yanar gizo wato website shi ne hanya mafi sauki da za ka tallata aiyukan ga dimbin jama’a. 

Zamani ya zo wanda kusan kowa na amfani da wayar sa ta hannu don binciko abin da ya ke bukata, kaman ta hanyar  amfani da manhajar Google, a misali. Mu kan binciko littafai, al’amuran yau da kullum, kasidu, kai har ma da kayayyakin masarufi a duniyar gizo sau da yawa domin mu san abin da ake yayi kuma mu samu bayanan da muke so. 

Shin kun taba tsayawa ku lura da abin da ke faruwa idan kuka binciko wani abu a Google? 

Abin da ke faruwa shi ne: shafukan yanar gizon da suka kunshi bayanai game da abin da aka binciko su ne za su bayyana  a sakamakon binciken. 

Misali: Idan na rubuta “Kayan Ado” na binciko a Google, to duk shafukan yanar gizon da suka kunshi bayanai game da kayan ado ne za su bayyana. 

To me zai faru idan na latsa daya daga cikin shafukan da suka fito a sakamakon binciken na Google? 

Zan fado cikin shafin yanar gizon wani mutum ne wanda shi ne ya wallafa bayanan game da kayan adon. Daga nan zan ga irin kayayyakin sa wanda ya ke tallatwa a shafin na sa, daga nan kuma idan na ga kayan da ya burge ni, zan nemi hanyar tuntubar sa domin sayan kayan, idan dama a shafin na sa akwai hanyar tuntuban, nan take zan same shi, mu kulla alakar kasuwanci. 

Ko me kake yi, ko min girma ko kankantar kasuwancin ka ko hajar ka, wani na nan zai binciko shi a intanet. Kuma idan ya bincika, mutanen da suka mallaki shafukan yanar gizon zai tarar, ko da kuwa hajar ka ya fi na kowa inganci. Idan dai har baka shiga duniyar intanet ba, to hakika kana rasa dimbin dama daga dimbin al’ummar da ke amfani da intanet din a kullum. 

Wannan daya kenan daga cikin tasiran shafin yanar gizo ga ‘dan kasuwa a wannan zamanin. Don haka yi kokari ka mallaki shafin yanar gizo don kasuwancin ka ya rika tafiya tare da zamani. 

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne wanda aka kirkire shi cikin harshen Hausa wanda ke bayar da daman mallakan shafin yanar gizo ga kowa cikin sauki kuma a kyauta. Manya da kananan kungiyoyi, makarantu, da ‘yan kasuwa na amfani da shi wajen kirkira da kuma sarrafa shafukan yanar gizon su. Wani babban abin burgewa ga wannan manhaja shi ne an tsara shi ta yadda za ka iya sarrafa shi daga wayar ka ta hannu. Ma’ana ba dole sai ka mallaki kwamfutar laptop ko desktop ba. Idan dai har ka mallaki adireshin Email kuma kana iya karanta sakonni ta Email din to za ka iya mallakan naka shafin yanar gizon ta hanyar ZamaniWeb. Ga masu sha’awar bude nasu shafin, sai ku ziyarci shafin mu na ZamaniWeb ko kuma ku rubuta www.zamaniweb.com

Idan kuna biye da mu, za mu ci gaba da kawo maku bayanai irin wandannan a game da shafin yanar gizo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =