Mabiya darikar shi’a ta IMN a Nijeriya sunsha alwashin fita a yau Talata domin yin jerin gwanon da suka sabayi duk ranar 10 ga watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci domin nuna bakin ciki da kisan Imam Hussain a yakin karbala.
A baya dai, gwamnatin Nijeriya ta haramta dukkan wasu ayyuka da jerin gwano da mabiya mazahabar shi’a keyi bayan wani fito na fito da kungiyar tayi da gwamnati wanda ya haifar da asarar rayuka.
Sai dai kuma kakin kungiyar Malam Ibrahim Musa ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya, zasu fito a dukkan sassan Nijeriya domin yin jerin gwano kamar yadda suka saba, duk kuwa da gargadin da rundunar ‘yan sanda tayi na jaddada haramcin dukkan ayyukan da kungiyar keyi.
A rikicin baya bayan nan da akayi a Abuja tsakanin kungiyar da jami’an tsaro, an samu mutuwar dan sanda guda daya da kuma fararen hula, inda wasu kuma suka samu raunuka.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bawa jami’anta umurnin dakile dukkan wani yunkuri na gudanar da muzaharar ta ‘yan shi’a mabiya Ibrahim Elzakzaky. Tuni dai aka baza jami’an yan sanda a manyan biranen Kano, Kaduna, Abuja da kuma sauran sassan kasar domin ganin an hana yin jerin gwanon da ‘ya’yan kungiyar ta IMN keson yi a yau Talata.
Babbar ayar tambaya a nan itace, shin mabiya mazahabar shi’a zasu bi wannan umurni da ka basu don zama lafiya ko kuwa zasu bijire kamar yadda suka sabayi a baya? Wane mataki ‘yan sanda zasu daukar idan aka karya dokan da suka bada? Wane irin daga za’a ja tsakanin mabiya zakzaky da jami’an tsaro? Zaman lafiya dai akace babu abinda ya kaishi dadi.
Akwai bukatar jami’an tsaro su sanya ido matuka ga dukkan abinda zai tada zaune tsaye domin kare rayuka da dukiyar al’umma. Dole shugabanni su rika tsawatawa mabiyanzu wajen ganin cewa basa daukar doka a hannu, sannan kuma dukkan dan kasa ya zama wajibi yayi biyayya ga dokokin kasa. Yin haka shi ne kadai hanyar da zata samar wa kasa da al’ummarta zaman lafiya ta re daci gaba.
Babu kasar da zata samu wani tagomashi ta harkan kasuwanci, da sauran al’amurra in har bata zaune lafiya. Zaman lafiya itace hanya daya tilo da zata samar da aikin yi ga ‘yan kasa, habaka tattalin arziki da samar da ababen walwala ga kowa.