Sako Ga Magoya Bayan Sanata Kwankwaso

76
Rabiu Kwankwaso

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Bayan gaisuwa nayi farin ciki da samun kaina cikin wannan tafiyar don haka ina son bayar da shawara a dukufa da addua wajen yakin neman kuri’a tun daga yanzu. 

Bayan haka a ci gaba da yayata ayyukan da mai girma sanata kwankwaso ya yi a baya, da Wanda yake yi a yanzu.

Kuma a lura da irin mutanen da ake muamala da su cikin wannan tafiyar. Saboda lokacin tafiyar Atiku an yi ta bude group da sunan sa ana yakarsa, na fahimci haka don idan mun ba da shawara ba godiya ba sharhi.

Kuma a lura da dalilan da suka kayar da Atiku na rashin yan jaridar kirki masu kareshi da yin ko oho da masu basu shawara sai son kudinsa.

Ganin irin himmata akwai wata ‘yar takarar gwamna  ta ACD a Bauchi Hajiya Baheejah Mahmoud ta dauki nauyi nayi ta program a radiyoyin Bauchi don tallata Atiku Kuma ya taimaka Amma saboda a sama basu San ana yi ba haka aka kare gwamnatin Buhari tayi abin da ta yi aka ce ya Fadi don haka a lura da wannan.

Tun yanzu ya kamata a dauki mikatin tafiyar kwankwaso a kafa kungiyar yakin neman zabe dabam dabam.

Akwai manyan dalilai uku da suka kayar da Atiku duk lokacin da kuke bukata zan fade su Don a kiyaye su a tafiyar kwankwaso.

Daga karshe Ina so a dauki wannan tafiyar da muhimmanci ta hanyar tabbatar da kowane mutum yana da akida ta gaskiya ba ta yaudara ba. Kuma a rika neman shawara ana sauke shawarar kan takarda ana nazari kuma a rika isar da su ga sanata kwankwaso don ya San mutanen da suke masa aiki bil hakki da gaskiya. Nagode Allah ya taimakemu sai naji raayinku.

Muazu Hardawa ya rubuto wannan wasika ne daga Bauchi 08062333065

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 5 =