Kwamitin kudi na majalisar dattawa zaiyi sammacin minister kudi da shugaban hukumar tattara kudaden haraji domin yi masu Karin bayani kan dalilin kara haraji da gwamnatin taryya ta amince dashi.
Shugaban kwamitin Solomon Adeola ne ya bayyana haka a cikin sanarwan da ya fitar jiya Alhamis a Abuja ta hannun mai taimaka masa kan kafafen yada labarai Kayode Odunaro.
Gayyatar da akayi masu dai ta ta’allaka ne akan shirin gwamnatin na kara kudin haraji da ga akshi 5 zuwa kasha 7.2
Minister kudi Zainab Ahmed dai ta sanar da shirin gwamnati na kara kudin harajin ranar Laraba bayan kamala taron majalisar zartarwa ta kasa a Abuja.
Adeola yace shirin Karin kudin harajin ya haifar da cece-kuce tsakanin al’umma musamman ma ganin yadda hakan zaiyi tasiri a rayuwarsu da kuma tattalin arzikin kasa.