Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya amince da nadin mutane 25 a matsayin masu bashi shawara, kamar dai yadda sakataren gwamnatin jihar Anthony Ijohor ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba a garin Makurdi.
A cikin wadanda gwamnan ya amince da nadin nasu akwai Emmanuel Manger, Abraham Abam, James Uloko, Nguman Agera, Adanu Sule, da sauransu.
Sanarwan tace a yau Alhamis ne Gwamnan zai rantsar da masu bashi shawaran.
Gwamnan kuma ya amince da nadin Emmanuel Aper a matsayin shugaban kumar bada ilimin bai daya na jihar Benue, yayinda Egli Ahubi, Mike Kusah, da James Ahua zasu kasance a matsayin mambobi.