Gobara ta lakume rayukan jarirai 8 a asibiti

120

Jarirai 8 ne hukumar tsaro ta kasar Algeria ta bayyana cewa sun kone kurmus sakamakon gobarar da ta tashi yau Talata a wani asibiti na kasar.

Hukumar tsaron ta bayyana cewa gobarar ta tashi ne da safiyar yau Talata a asibitin dake yankin Oued Souf mai tazarar kilomita 700 da kudu maso gabas na babban birnin kasar Algiers.

Jariran sun mutu ne sakamakon konewa da kuma shakuwar hayakin gobarar, sannan kuma an ceto jarirari guda 11 da wasu mutane 65 wadanda suka hada da mata 37.

Ko a shekarar 2008 sai da gobara ta tashi a asibitin inda tayi mummunar barnata mafi akasarin sashin asibitin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 4 =