Da Dumi-Dumi: Buhari da Atiku zasu san matsayinsu a gobe idan kotu ta yanke hukunci

89
Buhari da Atiku

Kotun dake sauraron karar zaben shugaban kasa ta sanya gobe Laraba don yanke hukunci kan shari’ar da takeyi tsakanin Muhammadu Buhari na jam’iyar APC da mai kararsa Atiku Abubakar na jam’iyar PDP.

A gobe Laraba 11 gawatan Satumba, wanda ya kasance sauran kwanaki biyar wa’adin sauraron karan yakare, kotun zata zauna domin yanke hukunci.

Atiku Abubakar da jam’iyarsa na PDP suna kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben da akayi masa cikin watan Fabarairu na wannan shekarar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + fourteen =