Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada kwamitin bashi shawara kan bukasa tattalin arzikin kasa.
A cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan yada labarai Femi Adesina ya fitar jiya Litini yace Buhari ya nada Farfesa Doyin Salami a matsayin shugaban kwamitin.
Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Dr. Muhammad Sagagi a matsayin mataimakin shugaba, sai kuma Dr. Mohammed Adaya Salisu a matsayin sakatare.
Sai kuma mambobin kwamitin wadanda suka hada da Bismarck Rewane, Prof. Chukuma Soludo, Dr. Iyabo Masha, Dr. Shehu Yahya da kuma Prof. Ode Ojowu.
A baya dai mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo ne ya jagoranci kwamitin bunkasa tattalin arzikin kasa a matsayin shugabanta.