Batun kin jinin baki a Afrika Ta Kudu

123

A cikin ‘yan shekarun nan da suka gabata dai, kasar Afrika ta Kudu mai yawan al’umma sama da miliyan 50 ta kara kaurin suna kan nuna kyama da tsangwama ga ‘yan kasashen ketare da basu wuce milyan 4 ba da ke rayuwa a kasar ta Afrika ta Kudu.

Tun kafin shekarar alal dubu daya da dari tara da casa’in da hudu (1994) baki ‘yan kasashen waje sun fuskanci kyama da tsangwama mara iyaka a hannaun al’ummar kasar Afrika ta Kudu, kuma irin wannan tsangwama zuwa yanzu sai kara Kamari yakeyi.

Abin bakin ciki da takaici shine yadda gwamnatin kasar taki tsawatawa da kuma daukar mataki mai tsauri kan ‘yan kasar da suke aikata wannan mummunar ta’asa ga ‘yan kasashen ketare, musamman ma al’ummar da suka fito daga tarayyar Nijeriya- Daga lokaci zuwa lokaci, ana kashe ‘yan Nijeriya a kasar Afrika ta Kudu tare da salwantar masu da dukiyoyinsu ta hanyar kone masu shaguna da sauran wuraren sana’a ba tare da sun aikata laifin zaune ko na tsaye ba.

Tun daga shekarar 2000 zuwa kusan shekarar 2008, a kalla an kashe ‘yan kasashen ketare da ke kasar Afrika ta Kudu kusan 67 tare da illata dukiyoyinsu, kuma babu wani kwakwaran mataki ko hukunci da aka dauka ga wadanda suka aikata hakan. Irin wannan mummunar halin yaci gaba da afkuwa tare da kuma kara muni a shekarun 2008, 2010, 2012 har zuwa shekarar 2017.

Masu wasoso na kokarin shiga shagunan baki a Afrika ta Kudu

Cikin yanayi na rudani da bacin rai a wannan satin, sai gashi an sake kai irin wannan hari na ta’addanci akan baki ‘yan kasashen ketare, inda a kalla mutane 3 ‘yan Nijeriya suka rasa rayukansu kamar yadda alkaluma suka nuna, kuma akayi hasarar dukiya na miliyoyin naira. Wannan hali na wasu daga cikin mutanen Kasar Afrika ta Kudu abin ayi tir da Allah wadai dashine, kuma hakan ba komai zai haifarwa kasar ba face tsamin dangantaka na diplomasiya tsakanin ta da sauran kasashen duniya indai har taki daukar matakan kawo karshen wannan rashin Imani da ‘yan kasarta ke aikatawa akan baki, da kuma hukuntasu.

Ya zama wajibi ga gwamnatin Nijeriya ta nemi diyya ga Afrika ta Kudu kan Kisan ‘yan Nijeriya da lalata masu dukiyoyi a rikicin kyamar baki da akayi. Akwai bukatar Shugaba Buhari ya sanya kwamiti mai karfi da zaibi Kadin lamarin tare da tabbatar da cewa anbima ‘yan Nijeriya hakkinsu. Tura manzo zuwa Afrika ta Kudu da gwamnatin tarayya tayi a jiya Alhamis don tattaunawa da shugaba Ramaphosa kan yadda za’a shawo kan lamarin kadai bazai isa ba, dole sai an dauki tsauraron matakai na ladabtar da duk masu hannu akan lamarin.

Ya kamata kasar Afrika ta kudu tasan cewa barin wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa ba tare da hukuntasu ba zai sake basu kwarin guiwa tare da sake aikita hakan nan gaba.

Lokaci yayi da ya kamata Kungiyar tarayyar Afrika, Majalisar dinkin Duniya da sauran manayn kasashe masu fada a ji da su tsawatawa kasar Afrika ta Kudu kan wannan ta’addanci da ‘yan kasarta ke aikatawa akan baki, tare da nuna masu illar cigaba dayin hakan. Tabbas za’a samu durkushewan kasuwanci, rashin zaman lafiya, mutuwar tattalin arziki da kuma tsamin dankanta da sauran kasashen duniya a Afrika ta Kudu in har mahukunta a birnin Johannesburg suka ki daukar matakin kai karshen hare-hare da ake kaiwa yan kasashen ketare a kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 + six =