MUJALLAR ‘THE ECONOMIST’ TA KASAR AMURKA TA SAKE HASASHEN CEWA BUHARI ZAI FADI ZABEN 2019!

136

Daga Kabir Ringim.
A karo na biyu cikin kasa da watanni biyu, mujallar masana tattalin arzikin nan ta kasar Amurka wacce ta shahara a duniya ta sake hasashen cewa Shugaba Buhari zai fadi zabe a 2019.
Mujallar wacce ta kware wajen hasashe akan zabuka da harkokin tattalin arziki, tsimi da tanadi a duniya bakidaya, tayi hasashen faduwar tsohon shugaba Goodluck Jonathan gami da nasara ga Buhari gabannin zaben 2015.
A wani rahoto wanda bangaren bincike da nazari na mujallar ya fitar akan Nigeria ranar 17 ga watan Oktoba na 2018, wanda jaridar Thisday ta gani, sun tabbatar da ingancin hasashen nasu.