GWAMNATIN NIGERIA ZATA FITAR DA MATSAYA AKAN MAFI KARANCIN ALBASHI RANAR LITININ

81

Daga Kabir Ringim.
Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya sanar da hakan ga manema labarai na fadar gwamnati yau Juma’a a Abuja. A baya dai ana ta sa’insa tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati inda ‘yan kwadago suka dage akan naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi yayinda gwamnatin tarayya tace naira 24,000 zata iya biya, jihoshi kuma suka amince da naira 20,000.
Kungoyoyin na kwadago sunyi yajin aikin gargadi kwanakin baya kuma sunyi barazanar komawa ranar 6 ga watan gobe muddin ba a amince da mafi karancin albashin da suke nema ba. Sai dai gwamnatin tarayya ta zartar da dokar ‘babu aiki, babu biya’ satin daya gabata.