YAN TAKARAR NEMAN SHUGABANCIN KASA SAMA DA 70 NE ZASU FAFATA A ZABEN 2019

31

Daga Kabir Ringim.
 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar da sanarwa cewa ‘yan takarar neman shugabancin kasa sama da 70 ne zasu fafata a zaben 2019.

Manya daga cikin yan takarar akwai shugaba mai ci, Muhammadu Buhari na jam’iyya mai mulki ta APC da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Sauran sun hada da mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC, sai tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ta jam’iyyar ACPN da Fela Durotaye na jam’iyyar ANN, da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

thirteen + 11 =

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.